1 Timothy 2

Umarnai A kan Sujada

1Da farko dai, ina gargaɗe ku cewa a yi roƙe-roƙe, ana adduʼoʼi, ana yin adduʼa a madadin waɗansu da kuma a yi godiya saboda kowane mutum—  2da sarakuna da dukan masu mulki, domin mu zauna lafiya, rai kuma kwance, muna bin Allah sosai a cikin natsuwa. 3Wannan yana da kyau, yakan kuma gamshi Allah Mai Cetonmu, 4wanda yake so dukan mutane su sami ceto su kuma zo ga sanin gaskiya. 5Gama Allah ɗaya ne, matsakanci kuma ɗaya tsakanin Allah da mutane, shi ne kuwa Kiristi Yesu, 6wanda ya ba da kansa fansa domin dukan mutane-shaidar da aka bayar a daidai lokaci. 7Don haka ne aka sa ni mai waʼazi, da manzo kuma -gaskiya nake faɗa, ba ƙarya ba-na kuma zama malami mai koya wa alʼummai alʼamarin bangaskiya da kuma na gaskiya.

8Ina so maza a koʼina su ɗaga hannuwansu masu tsarki cikin adduʼa, ba tare da fushi ko faɗa ba.

9Ina kuma so mata su lura su yi wa kansu adon da ya cancanta, da rigunan da suka dace, ba da adon kitso ko sa kayan zinariya ko luʼuluʼu ko kuma tufafi masu tsada ba, 10sai dai su yi ayyuka masu kyan da suka dace da matan da suke masu bauta wa Allah.

11Ya kamata mace ta riƙa koyo cikin natsuwa da cikakkiyar biyayya. 12Ban ba mace izini ta koyar ko ta yi mulki a kan namiji ba; sai dai ta zauna shiru. 13Gama Adamu ne aka fara halitta, saʼan nan Hawwaʼu. 14Ba kuma Adamu ne aka yaudara ba; macen ce aka yaudara ta kuma zama mai zunubi. 15Amma mata
Da Girik ita
Za ta sami ceto
Ko kuwa maido
za su sami ceto ta wurin haihuwa-in suka ci gaba cikin bangaskiya, ƙauna da kuma tsarki tare da halin sanin ya kamata.

Copyright information for HauSRK